Darakta Janar na kungiyar bada agaji ta Action Aid a Najeriya Misis Ene Obi ta bukaci gwamnatin tarayya ta lashe amanta na haramta amfani da shafin tuwita a Najeriya.
Obi ta ce matsalar tsaro da tattalin arziki ya kamata gwamnatin ta fara haramtawa ba wai zuwa ta huce fushin ta kan yan kasa a bangaren tuwita ba.
Daraktat ta yi wannan batu ne a birnin tarayya Abuja yayin wani taron fasahar zamani na wata kungiyar matasa.
Ta ce shafin tuwita na da matukar muhimmanci ga rayuwar dan Najeriya, don haka ne take kura da gwamnatin tarayya da ta lashe amanta.