Shugaba Muhamamdu Buhari ya kaddamar da aikin gina masana’antar sarrafa iskar gas ta Najeriya ta bakwai, yana mai bukatar a kammala aikin a kan lokaci domin a fara ta 8.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin wani taro ta na’ura da ya gudana a ranar talata, da ya zo daidai da bikin kaddamar da aikin Bonny Island dake Jihar Ribas.
Shugaban kasar ya kuma ja hankalin shugabannin gudarwar kamfanin, da gwamnatin jiha da ma al’ummar yankin, da kada su bari aikin ya ɗaiɗaita don samun moriyarsa.
“Kamar yadda muke kaddamar da wannan aiki a yau, ina fatan nan gaba kaɗan za mu kara kirkiro da wasu inda jama’a da dama za su amfana” cewar Buhari.
“Kazalika zan yi amfani da wannan dama wajen yaba wa masu bada tallafi na kasashen duniya bisa namijin ƙoƙarin su, kuma gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen alkinta ayyukanta”
Da yake tofa albarkacin bakinsa, ministan albarkatun man fetur Tymipre Sylva, ya jinjina wa kokarin gwamnatin tarayya, inda ya yi alkawarin cewa ma’aikatar ba za ta bada kunya ba.