Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya salon sauya tsarin fasalin kasarnan da wasu ke hankoro na kan turba, don haka shi ma yana goyon baya dari bisa dari.
Har wa yau gwamna Fintiri ya ce muddin sauya fasalin kasar zai taimaka wajen gyaran targaden da kasar nan ke fama da shi, to babu shakka matakin aiwatar da hakan shine Alkhairi.
Da yake magana a yayin kaddamar da Asibitin kwararru mai daukan gadaje 220 dake birnin Asaba, Fintiri ya yaba da tsarin gudanar da mulkin gwamnan Jihar ta Delta Ifeanyi Okowa ta inda har yake kawo musu romon Dimokuraɗiyya.
“Babu shakka akwai abubuwa dake damun kasar nan, wanda suka kai ga wasu na kira ga ɓallewa, ama idan aka dauki mataki lallai za a iya magance” cewar Fintiri.
Da yake maida jawabi gwamnan jihar Delta Dakta Ifeanyi Okowa, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da aiwatar da dokar kiwon lafiya ta kasa, don rage yawan mace macen mata masu haihuwa.
A cewarsa, baya ga inganta tsarin harkokin mata masu haihuwa, Shirin zai taimaka gaya wajen farfado komadar tattalin arziki.