Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta baje kolin wasu mutun 60 da Wani matashi bisa zargin kai hari ga jami’an ta, da kayayyakin ta, da kuma wasu laifuffuka.
Lokacin da ya ke jawabi a wurin baje kolin wadanda ake zargin, Kwamishinan yan sandan jihar Aliyu Garba ya ce, mutun 50 daga cikin wadanda ake zargin na da hannu dumu-dumu, a kai wa jami’an ta hari, da kuma kayayyakin gwamnati a fadin jihar.
Garba ya ce, ansami bindigu kiran AK-47 da harsasai masu kisa, kananan bindigu kiran gida, wukake, layoyi, da dai sauransu, a hannun wadanda ake zargin.
Kwamishinan ya kara da cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, mai suna Daniel Elon mai shekara 17, ya tabbatar da cewa, ya na daya daga cikin masu tsara kai hare hare a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari ya amince da gina sabbin jami’o’i biyu a Najeriya
Matashi ya Kuma ce, “Gun-gun na su ne, ke da alhakin kai hari a ofishin yan sandan da ke garin Abakaliki, lokacin zanga zangar #EndSARS da ya gudana a shekarar 2020, inda aka kashe wani jami’in dan sandan mai mukamin Insfecta ” inji shi.
A karshe kwamishinan ya kuma ce, an duba wasu harsashan bindiga kirar AK-47 da aka samu a hannun wadanda ake zargin, kuma an tabbatar da iri daya ne, da na jami’in Insfectan da bata garin suka kashe, a cewar sa.
Comments 1