Zamu tallafawa Noma a Arewa wasu daga cikin Manyan Kasashen Turawa
Gwamnatin Kasar Canada da Hadaddiyar Kungiyar Turai ma tallafawa Kasashen Afirika da Gwamnatin Kasar Jamus da Masarautar Kasar Norway da Masarautar Kasar Sweden na hada kudade don tallafawa Noma a Arewacin Kasar Najeriya.
KARANTA:- Jam’iyyar APC ta Karama Mai Mala Buni Wa’adi
Hada kudaden dai anayin shine ta hannun wata Kungiya mai suna Food and Agriculture Organization FAO wadda majalisar dinkin duniya ke da ita zata tallafawa manoma kimanin 65,800 dake zaune a Yankin Borno da Adamawa da Yobe wadda ta’adancin Yan bokoharam ya raunata.
A ranar Juma’a ne Kungiyar ta fidda wani bayani tana cewa ana samun tsaiko wajan noma da samun abinci a Najeriya, zata tabbatar da kawo kayan abinci musamman ga manoma masu karamin karfi.
Kungiyar tace duk da yaki a yankin samar da abinci zai kawo zaman Lafiya da samun kwanciyar hankali, shiyasa wannan Kungiya zata tallafawa manoma 65,800 dake Borno da Adamawa da Yobe, wanda kimanin manoma 40,000 zasu fito daga jahar Borno ne inda Kungiyar zata basu iri da kuma taki.
Kamar yadda kungiyar ta bayyana wannan shine karo na shida na tallafin da takeyi kan noma wadda Kungiyar tayi a jahohin uku, ba don kamai ba sai dan jahohin uku suna cikin rikici tun da dadewa.
Kungiyar tace tallafin wannan shekarar ta 2021 kungiyoyi da kashe irin su Gwamnatin Kasar Canada da Hadaddiyar Kungiyar Turai ma tallafawa Kasashen Afirika da Gwamnatin Kasar Jamus da Masarautar Kasar Norway da Masarautar Kasar Sweden suka hada kudaden don tallafawa.
Comments 1