Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa illar da Shaye-shaye ke yi a Najeriya ta fi ta matsalar tsaro muni a Najeriya.
Shugaba Buhari ya fadi haka ne a ranar Asabar yayin kaddamar da shirin yaki da matsalar shaye shaye da ya gudana a fadar shugaban kasa.
Kuma wannan taro ya zo ne daidai da ranar da majalisar dinkin duniya ta ware don yaƙi da matsalar kwankwadar miyagun kwayoyi da safararsu.
Shugaba Buhari wanda Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya wakilta, ya umarci hukumar dake hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA da ta gaggauta janyo al’umma a jiki don bada gudummawar du wajen yaƙar matsalar.
Kazalika ya umarci hukumar da ta tsananta bincike lungu da sako don bankado maboyar mashaya da ma gonakin taba wiwi a fadin kasar nan musamman yankin Kudancin kasar da lamarin ya fi kamari.