Osinbajo ya Jagoranci hadin guiwa da majalisar dinkin duniya wajan wadata abinci a Najeriya.
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya Jagoranci gwamnatin tarayyan Najeriya da majalisar dinkin duniya wajan tabbatar da abinci ya wadata a Najeriya, wannan na daga cikin kudirin shugaban kasa Muhammadu Buhari da yace zai fidda Yan Najeriya miliyan dari daga talauci. Jaridar Tvcnews ta ruwaito
KARANTA:-Gwamanatin tarayya ta sanar da cafke Nnamdi Kanu
Wannan wani yunkuri ne na rake radadin yunwa da cututtukan da rashin wadatar abinci ke haifarwa.
Gwamnatin tarayya tare da majalisar dinkin duniya sun gabatar da taruka daban-daban a cikin kasar Najeriya dama wadansu gurare kan yadda za’a wadata abinci a sassa guda shida daban-daban dake Najeriya.
Farfesa Osinbajo ya gabatar da kudirin ne a Abuja inda suke tattaunawa da wasu daga cikin wakilan majalisar dinkin duniya wanda wasu daga cikin gwamnoni suka halatta, sannan sakatariyar majalisar dinkin Amina Muhammad na daga cikin wadanda suka zauna, sannan da wasu manya-manya daga wasu bangarori daban-daban.
Kamar yadda mataimakin Shugaban Kasa yace” gwamnatin tarayya Najeriya na matukar kokari wajan ganin an wadata abinci a kasar, wanda hakan na daya daga cikin manyan hanyoyi da za’abi wajan fidda mutane daga talauci.
Daga cikin manyan da suka halarci taron sun hada da minista harkokin noma da raya karkara Alhaji Muhammad Nanono, Dr. Osagie Ehinare, da Hajiya Zainab Ahmada da Alhaji Lai Muhammad da Price Clem Agba da kuma wadda ta hada taron Misis Olusola Idowu.
A cikin taron kuma Farfesa Kola Amigo daga jami’ar Ahmadu Bello dakeZaria ya gabatar da wani bincike daya samo a tarukan da majalisar dinkin duniya ta gabatar a kasar kan habbaka abinci, sannan wasu daga cikin yaran Najeriya sunyi magana a kai.