Majalisar wakilan tarayya ta gayyaci shugaban hukumar kayyade farashin man fetur ta kasa PPPRA wato Abdulkadir Sa’idu da ya zo ya mata bayani dalla-dallah kan batar dabon da naira biliyan daya da digo shida biyu ya yi.
Shugaban Kwamitin Majalisar kan harkokin kudi James Faleke shine ya bukaci hakan yayin sauraron bahasi game da wani liki da ya taso har dala biliyan 30 na kudaden shiga na shekara shekara.
Faleke ya ce wannan gayyata da aka yiwa shugaban PPPRA ya zamo wajibi domin hakan ne zai bada damar jin yadda aka yi kudaden suka yi batar dabo ba tare da shiga asusun tarayya ba.
Ya kar da cewa allura ce za ta tono garma, domin kwamitin zai tada batun ne tun daga shekara ta 2012 kana kuma dole ne sai am sany kudaden a asusun tarayya ko an ki ko an so.
Har wa yau ya ce dole ne hukumar ta PPPRA ta bankado wanda ta bashi ramce wannan kudade kana ka a samu takardar amincewa daga akanta Janar na tarayya.
Domin a cewarsa babu ta yadda za a yi ba gaira ba dalili wani kawai ya wawushi kudi daga asusun tarayya ba tare da izni ba.
Kawo yanzu dai Shugaban Hukumar PPPRA Abdulkadir Sa’idu ya gaza bayyana gaban majalisar don amsa tambayoyi.