Gwamanatin tarayya ta sanar da cafke Nnamdi Kanu
Babban kotun Najeriya dake Abuja ta sanar da cafke Jagoran masu fafutukar kafa kasar BIAFRA Nnamdi Kanu inda tace yana garkame a ofishin Jami’an tsaro na sirri watau DSS. Jaridar Vanguard ta wallafa
Mai Shari’a Binta Nyanko ta bada umarnin tsare Kanu wanda jami’an hadin guiwar kasa da kasa suka Cafke shi a Kasar waje, da ya cigaba da zama a garkame har sai ranar ashirin da shida ga watan July domin cigaba da Shari’a.
KARANTA:-Akalla Jagorori 50 aka koyar kan yadda zasu shawo kan matsalar cin mutunci mata da yara a Sokoto
An cigaba da zaman kotun Jim kadan bayan shugaban Alkalin Alkalai ya sanar da cafke Nnamdi Kanu ga manema labarai.
Yace ana tuhumar Namdi Kanu da manyan laifuka da suka hada da ta’addanci, hada kai wajen yima gwamnati tawaye, samun makamai ba tare da izini ba tare da Jagorantar wani yanki ba tare da izini ba.
Ya Kara da cewa maganganun da yake fada ne suka jawo rushe rushe da kuma rasa rayuka da akeyi a kudanci Kasar.
An rako Jagoran masu fafutukar kafa kasar BIAFRA Nnamdi Kanu har zuwa Kotu a ranar Talata tare da jami’an Yan sanda da na DSS da yawa.
Idan baku manta ba a wancan zaman da akayi a Kotu a ranar 28 ga watan May na shekarar 2019 an bada damar kamashi bayan soke belin da aka bashi.
Shi dai Jagoran IPOB mai shedar zaman kasa kala biyu kamin a kamashi a ranar Lahadi an sanar da ganinshi a gurare da kasashe daban-daban in da suka hada Jerusalem da kuma United Kingdom.