• Sanata Kabiru Marafa ya ce, mutun zai iya shigowa jam’iyar da mukamin shi Amma daga baya, ya rasa.
• Marafa ya bayyana hakan ne a wani Taron gaggamin da ya gudana a jihar.
• Ya Kuma shawarci masu ruwa da tsaki da su yi duk mai yiwuwa wajan ciyar da jihar gaba.
Sanata Kabiru Marafa na jam’iyar APC daga jihar Zamfara ya bayyana cewa, Jami’iyar fa tamkar farar ta kadda ce, akan injin Foto Kofi, asaka farar takadda sal tafito da rubutu daga baya.
Sanata Marafa ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a wani Taron gaggamin magoya bayan jam’iyar, daya gudana a jihar Zamfara.
Inda ya ce, Mutun zai iya barin wata jam’iyar ya na da mukami, amma ya shiga cikin jam’iyar ta APC ya kuma rasa wannan mukamin nasa” inji shi.
Sai dai kafin wannan zance Sanatan sai da ya yi wa daukacin sabbin shiga jam’iyar barka da zuwa wacce ya kira da ta tsakanin da Allah.
Ya kuma Kara da cewa, “Duk wadanda zasu shigo jam’iyar a yanzu zasu shigo ne da mukamin su, kuma a talakance, inda zamu aje masu benci da ga gefe, domin su zauna”.a cewar sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya ta ya ba wa Hukumomin tsaro
A karshe Sanata Kabiru Marafa ya kuma shawarci masu ruwa da tsaki dake jihar ta Zamfara, dasj zauna, su yi duk mai yiwuwa wajan ciyar da jihar gaba.
Comments 1