• Ministan Mai, da Mele Kyari suna ganawar da majalissar dattijan kasar nan.
• Ana dai saran cewa, zasu tattauna ne akan kudurin Man Fetur.
• Tun a jiya labarai ce dai, Shugaban majalissar ya tsegwan tawa takwarorin shi zuwan mutane biyun.
A yanzu haka Majalissar dattijai na wani ganawar sirri da Ministan albarkatun Mai na Kasa Timipre Sylva, da kuma Babban Daraktan kamfanin matatar Mai na Kasa, NNPC Mele Kyari.
Mutanan biyu sun je majalissar ne karkashin jagorancin Babban mai bai wa Shugaban kasa Shawara a kan harkokin majalissar Dattijai Sanata Babajide Omoworare, inda ake kyauta zaton cewa, zasu yiwa majalissar bayani ne, akan kudirin Man Fetur na PIB, Wanda ake saran Sanatoci zasu tabka muhawara a kan shi bayan taron.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalissar Dattijai ta amince da kudurin da Sanata Uba Sani ya gabatar.
Tun a jiya laraba ce, Shugaban majalissar Dattijai na Kasa Sanata Ahmad Lawan, ya tsekunta wa majalissar cewa, Slyva da Kyari zasu ziyarci majalissa a wani sa’a na yau Alhamis, domin yin cikakken bayani akan kudirin PIB ga Sanatoci.
Kwai Karin bayani anjima, Idan Allah ya yadda……