Hukumar Jami’an tsaron farin kaya ta DSS ta ce jami’an dake tsaron kasurgumin dan ta’addan nan na yankin Yarbawa Sunday Igboho ne suka harzuka jami’an hukumar har suka faɗa musayar wuta.
A ranar Alhamis ne dai jami’an DSS din suka yi dirar mikiya a gidan Igboho dake birnin Badun inds kuma aka yi amannar cewa tuni suka yi gaba da shi.
Kakakin Rundunar DSS Peter Afunanya shine ya tabbatar da hakan bayan da jami’an DSS tare da hadin gwiwar karin wasu jami’an tsaro suka cika hannu da mayakan Igbohon har goma sha uku.
Wannan dirar mikiya kamar yadda Afunanya ya bayyana, ya biyo bayan wasu bayanan sirri ne da aka samu cewa Mayakan Sunday Igboho na amfani da karfin bindiga wajen kawo hargitsi a yankin kudu maso yammacin kasar nan.
Daga mutane sha ukun da aka kama, sha biyu maza ne yayin da kuma dayan ta kasance mace.