Gwamnatin tarayya ta ce ta yi amfani ne da salo iri daban-daban har ta samu nasarar sake cafke shugaban kungiyar Inyamurai ta IPOB wato Nnamdi Kanu tare da maida shi gida Najeriya.
Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammad shi ya fadi hakan yayin tattaunawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Lai Muhammad ya ce Najeriya ta yi amfani ne da dabaru irin na jami’an tsaro ciki da na waje da kuma hadin gwiwa da kasashen waje dake da dangantaka da wannan al’amari.
Ko da yake Ministan bai bayyana wadannan kasashe ba, amma ya ce Kasar nan ba za ta yi wasa da wannan dangantaka ba.
Duk da cewa yanzu haka ana cu gaba da gudanar da bincike kan Nnamdi Kanu, amma Lai Muhammad ya ce duk wanda ke da hannu wajen daure masa gindi toh gwamnati za ta yi maganinsa.