Tsohon dan wasan Najeriya Victor Moses ya yi bankwana da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar Ingila bayan shafe shekara 9 yana fafata mata wasa.
Yanzu haka Moses ya hade da kungiyar Spartak Moscow ta kasar Rasha.
Da ma dai dan wasan ya shafe kakar 2020/2021 yana a matsayin aro a kasar ta Rasha, zaman da ya fafata wasanni 20 a kakar da ta gabata.
Moses ya buga wasanni 128 a iya zamansa a Stamford Bridge bayan da hadwwa da ita a 2012 daga Wigan.