Rundunar sojin Najeriya ta ce a shirye take a yanzu haka don sake maido doguwar dangantakar dake tsakanin ta da fararen hular kasar.
Rundunar Sojin ta kara da cewa za ta iya sadaukar da komai nata don shiga lungu da sakon kasar da zummar kare rayukan yan kasa.
Kwamandar dake kula da rundunar sojin Najeriya ta takwas masu kare al’umma a Jihar Sokkwato Birgediya Janar Chinedu Ralph Nnebeife shine ya yi wannan alwashi yayin da ya jagoranci rundunar a wani aikin gayya da ya gudana a barikin soji na Giginya dake Jihar.
Ya ce sojojin kasar nan na jin daɗin dangantaka da fararen hula, don hala za su yi duk mai yiwuwa don sake dawowa karsashin su a idanun jama’a.
Birgediya Janar Chinedu ya kara da cewa hakan zai matuƙar taimakawa musamman ta fuskar yaki da ta’addanci da ake yi a fadin kasar.
Daruruwan sojoji ne suka fito kan tituna don gudanar da wannan shara tun daga barikin sojin na Giginya har suka karade kauyukan Domboa da Kwanawa dake karamar hukumar Dange/Shuni ta jihar Sakkwato.
Wannan aikin shara na zuwa ne daidai bikin ranar sojoji da ake gudanarwa kowacce shekara.