Kasurgumin dan ta’addan Kasar Yarbawan nan Sunday Igboho ya bayyana cewa babu wani jami’in tsaro da ya isa kamashi ko kum musguna mishi.
Kazalika Igboho ya sha alwashin cewa idan yan sama da dubu za su dunguma zuwa gidansa, to lashakka dakyar a samu 100 su fito da rai.
A wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar Litinin, Igboho ya ce su ma darin da za su fito din za su fito ne ta hanyar siddabaru ba wai haka kurum ba.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ne dakarun yan sanda suka yi dirar mikiya a gidan Igboho inda suka hallaka mutane biyu daga masu kula da tsaronsa yayin wani bata-kashi.
To sai dai daga bisani an ruwaito cewa Igboho ya tsallake fadawa komar jami’an tsaron, ko da yake sun bukace shi da ya gaggauta mika kai bori ya hau.