A yunkurin samun hanyar magance matsalar tsaho da ya addabi kasar nan, da ya hadar da: garkuwa da mutane, ta’addanci, tada bama-bamai, da kuma wasu manyan laifuka, Sarkin Musulmi Kuma Shugaban majalissar koli ta harkokin addinin Musulunci Alhaji Sa’ad Abubakar, Limamai, manyan malaman addinin Musulunci, da kuma wasu al’umar Musulmai dake fadin kasar nan, sun gudanar da addu’o’i na masamman a babban masallacin Kasa dake babban birnin tarayya Abuja a jiya Litinin, domin samun dauki daga wajan Allah madaukakin sarki.
Hukumar kula da ilimin harshen karancin da na addinin musulunci ta kasa NBAIS, tare da hadin gwuiwar gidauniyar AL-ANSAR, su ka shirya wannan Addu’o’i na musamman, a taron shekarar 2021, inda suka bukaci al’umar Musulmai da su yi Sallah raka’a biyu da kuma karanta wasu ayoyu a cikin Al’Qur’ani Mai gimar, domin rokon Allah da ya kawo karshen matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta.
Lokacin da ya ke jawabi bayan ya jagoranci sallar La’asar a Babban masallaci kasa da ke Abuja, Farfesa Shehu Galandachi ya ce, hakan na da matukar amfani ga Musulmi Dan Naijeriya, da karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar da ya roki Allah, a kan magance dukkannin matsalolin da ke fuskanta kasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: NFIU ta Kori Jami’an ta sabida binciken Atiku da Tinubu
“Muna rokon Allah da ya magance mana dukkannin matsalolin kasar nan, kamar ta’addancin kungiyar Boko Haram, Garkuwa da mutane, kashe-kashe Mutane, da kuma annobar cutar Korona, don haka abu ne Mai matukar anfani, ace Muntaru a wannan masallaci, domin yiwa kasa addu’a a kan samun saukin wadannan matsalolin” inji shi.
” Allah kadai zai iya magance mana wadannan matsalolin da muke fuskanta, don haka Muna rokon shi da ya magance mana su” a cewar Galandachi.
Ana shi bangaren lokacin da yake jawabi ga manema Labarai, Mukaddashin shugaban hukumar ta NBAIS, Farfesa M.S Abdullahi ya ce, Taron na yiwa kasa addu’o’i, na daya daga cikin taruka na shekarar 2021 da hukumar ta shirya, domin rokon Allah da ya maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasa Naijeriya.