Sashin bin ciken sirri kan madakatar kudi wato NFIU ta ta Kori wasu manyan jami’an ta biyu da ta dakatar kwanakin baya, a kan binciken Atiku Abubakar da Bola Tinubu.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, Shugaban hukumar NFIU na kasa, Modibbo Tukur, ne ya sanar da Koran wadandan ma’aikata biyu, a cikin takarda daya aike su.
Kazalika Tukur ya dakatar da wadannan jami’an ne tun a ranar watan Ogustan shekarar 2020, inda daga bisani ya rubuta wa jami’an wasikun sallama daga aikin a ranar 29 ga watan Yuni, 2021,
Wadanda aka sallama sun hada da: Mohammed Mustapha da Fehintola Salisu wadanda sun kai matsayin mataimakin darekta sun rasa aikin su ne, saboda sun Kirikiri wani bincike kan Bola Tinubu thsohon gwamnan jihar Legasa da Atiku Abubakar Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Kamar yadda Shugaban NFIU ya bayyana,
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari ya mika Tutar APC ga Matawalle
Modibbo Tukur ya zargi ma’aikatan da wasu laifin, amma ana tunanin babban abin da ya sa aka kore su shi ne, sun taba wadan nan manyan mutane yan siyasan.