Gwamnan jahar Borno Babagana Umara Zulum ya misanta zancen da ake yawo dashi na batun kafa gwamnati da ISWAP da Bokoharam sukayi, gwamnan yace ba gaskiya bane.
Gwamnan yace shine ke da ikon a kowane sassa na Jahar, babu wata sabuwar gwamnati da aka kafa wadda ba tashi ba. Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ya kammala tattaunawa da shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Abuja,.
KARANTA:- BABBAR MAGANA: Gwamnatin tarayya ta ware biliyan 4.8 don bin diddigin masu yin WhatsApp
Idan baku manta ba Yan kwanakin baya kadan ake yawo da zacen nada Abba Kaka a matsayin sabon gwamnan ISWAP a Jahar ta Borno.
Gwamna Zulum yace sam wannan ba haka yake ba, yace “har yanzu bamu tabbatar da zancen da ake yadawa na kafa gwamnatin ISWAP, Kuma a matsayina na gwamna bai kamata nayi magana akan abunda banda cikakken masaniya akansa ba.”
An tambaye shi ko yanada Shirin bin diddigin labari, sai dai cewa yayi bashi da nufin hakan.