Hukumomin Kasar Madagascar sun cafke wasu bakin haure da Yan asalin kasar kan yunkurin hallaka shugaban Kasar Madagascar Andry Rajoelina.Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Antoni Janar Berthine Razafiarivony ya bayyana cewa an fara cafke sune tun ranar Talata da aka fara bincike bayan jin rahotan yunkurin hallaka shugaban Kasar Madagascar.
Razafiarivony, yace anyi nufin hallaka shugaban Kasar Madagascar ne tare da wasu manyan Yan Siyasa dake Kasar.
KARANTA:- Wata sabuwa: Manyan jiga jigan jam’iyyar PDP guda 4 a Rivers sun koma APC
Babu wani alaman shaidar zama cikin kasar Madagascar cikin bakin hauren da aka kama.
An rantsar da shugaban Kasar Madagascar Rajoelina a 2019, bayan an kai ruwa rana tare da abokin hamayyar sa.
A wani labarin,
Manyan Jagororin jam’iyyar PDP hudu sun koma APC tare da magoya bayansu
Manyan jagororin jam’iyyar adawa ta PDP tare da magoya bayansu a karamar hukumar Khana dake Jahar Rivers sun koma jam’iyyar APC.
Mutanen sun hada da tsohon Sakataren karamar hukumar ta Khana, Hon. Dumka Philip Rojas, tsohon shugaban Yan majalisu na Karamar hukumar Khana, Hon Lekia Nwanikpo, tsohon mai lura da ayyuka na Karamar hukumar ta Khana, Hon Dumbete Obegu da kuma tsohon mai baiwa shugaban Karamar hukumar ta Khana shawara Hon. Dum Ntor-ue.
Tsohon Ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, yayin da yake karbar su a babban Ofishin shugaban Jam’iyyar APC na Jahar Engr Chukwudi Dimkpa, ya yabawa Jagororin jam’iyyar PDP kan sauya shekar su.
Dimpka, yayi musu alkawari tafiya tare dasu, da kuma basu dama wajan shugabancin jam’iyyar a kowane mataki.
Mai magana da yawun masu sauya shekar tsohon Sakataren karamar hukumar ta Khana, Hon. Dumka Philip Rojas, yace sun yanke shawarar barin jam’iyyar ta PDP ne duba da irin yanayin mulkin jam’iyyar a Jahar.
Rojas, ya kara da cewa sunyi sha’awar dawowa jam’iyyar ta APC ne duba da irin manyan ayyukan da cigaba da aka samar a Jahar ta Rivers.