Iyom Josephine Anenih, tsohuwar Ministan Mata, ta shawarci Mata dake cikin wannan kasa da su fito don neman mutane a zaben shugaban kasa da na gwamnoni da sauran kujeru. Kamar yadda Jaridar Dailytrust ta wallafa a shafinta
Anenih, tayi wannan batun ne a wajan taron karawa juna Ilimi, wanda kungiyar Dinidari da hadin guiwar Heinrich Boll Stiftung suka hada, a lokacin da take magana a kan wani batu mai taken “Daga titi sai dakin Majalisa, don karfafama mata wajan fitowa neman kujeru daban-daban a zabe mai zuwa a fadin kasar nan.”
KARANTA:- Gwamna El-Rufa’i ya bayyana HH Danjuna Barde a matsayin mai Samar da zaman lafiya
Tace “Na sha gayawa matasa Yan mata su shiga ana damawa da su, su fita a san su, babu tayadda za’ayi suci nasara idan basa shiga ana damawa dasu.”
“Kuje ku fafata da maza, za kuma ku sami nasara, yanzu wannan babban dama ne ga Matan Najeriya da su fito a dama dasu a siyasa, sunemi takarar kujeru daban-daban a fadin kasar nan.” Kamar yadda ta ayyana
Lokacin da Jagoran APC ta Mata Stella Okotete, ke magana cewa tayi za’a iya samun daidaiton maza da Mata a siyasa idan akwai kudade.
Oketete tace Matukar babu Yan kudade to tabbas ba za’a sami daidaiton mata ba a cikin shugabancin Kasar nan, sai dai muna iya sauya batun ya koma Mata sun fito baki daya su marawa mata Yan uwansu baya.
A wani labarin,
SIYASA: Zamu fidda gwarzon Dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, APC ga PDP
Jam’iyyar APC mai jagorancin kasa, ta sha alwashin fito da Dan takara nagari kuma mai farin jinin al’umma a babban zabe mai zuwa a shekarar 2023.
John James Akpanudoehede, Sakataren Jam’iyyar ta APC ya bayyana haka a ranar Laraba a garin Abijat.
Ya fadi hakane biyo bayan zargin da jam’iyyar adawa ta PDP ta keyi, kan cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin gadar da kujerar shugabancin Kasar nan ne.
Comments 2