Manyan jagororin jam’iyyar adawa ta PDP tare da magoya bayansu a karamar hukumar Khana dake Jahar Rivers sun koma jam’iyyar APC.Kamar yadda Jaridar Leadership ta wallafa a shafinta
Mutanen sun hada da tsohon Sakataren karamar hukumar ta Khana, Hon. Dumka Philip Rojas, tsohon shugaban Yan majalisu na Karamar hukumar Khana, Hon Lekia Nwanikpo, tsohon mai lura da ayyuka na Karamar hukumar ta Khana, Hon Dumbete Obegu da kuma tsohon mai baiwa shugaban Karamar hukumar ta Khana shawara Hon. Dum Ntor-ue.
Tsohon Ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, yayin da yake karbar su a babban Ofishin shugaban Jam’iyyar APC na Jahar Engr Chukwudi Dimkpa, ya yabawa Jagororin jam’iyyar PDP kan sauya shekar su.
KARANTA:- Zaben 2023: Mata su fito a fafata dasu a takarar kujerar shugaban kasa da Gwamnoni
Dimpka, yayi musu alkawari tafiya tare dasu, da kuma basu dama wajan shugabancin jam’iyyar a kowane mataki.
Mai magana da yawun masu sauya shekar tsohon Sakataren karamar hukumar ta Khana, Hon. Dumka Philip Rojas, yace sun yanke shawarar barin jam’iyyar ta PDP ne duba da irin yanayin mulkin jam’iyyar a Jahar.
Rojas, ya kara da cewa sunyi sha’awar dawowa jam’iyyar ta APC ne duba da irin manyan ayyukan da cigaba da aka samar a Jahar ta Rivers.
A wani labarin,
Zaben 2023: Mata su fito a fafata dasu a takarar kujerar shugaban kasa da Gwamnoni
Iyom Josephine Anenih, tsohuwar Ministan Mata, ta shawarci Mata dake cikin wannan kasa da su fito don neman mutane a zaben shugaban kasa da na gwamnoni da sauran kujeru.
Anenih, tayi wannan batun ne a wajan taron karawa juna Ilimi, wanda kungiyar Dinidari da hadin guiwar Heinrich Boll Stiftung suka hada, a lokacin da take magana a kan wani batu mai taken “Daga titi sai dakin Majalisa, don karfafama mata wajan fitowa neman kujeru daban-daban a zabe mai zuwa a fadin kasar nan.”
Comments 1