• Basaken jihar Kaduna da yan bindiga su ka yi Garkuwa da shi, ya shaki iskar yanci.
• Yan bindigan dai sun yi garkuwa da basaraken ne, a garin Panda na jihar Nasarawa, bayan ya ziyarci gonar shi.
• Basaraken Mai shekaru 83 na daya daga cikin Sarakunan mafiya yawan shekaru a jihar Kaduna.
Danladi Gyet Maude Mai rike da sarautar Gargajiya a jihar Kaduna, wanda Yan bindiga su ka yi garkuwa da shi a jihar Nasarawa, ya shaki iskar yanci.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda a ka yi garkuwa da basaraken, lokacin da ya jiyarci gonar shi, dake yankin Panda na jihar Nasarawa.
Amma wani Shaida ya bayyana wa Daily Trust a jiya Laraba cewa, an saki basaraken ne, da misalin karfe 9:30 na dare.
Sai dai shaidan bai bayyana cewa, ko an biya kudin fansa ba, kafin sakin Basaraken.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kebbi za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 36 a jihar
Basaraken mai shekaru 83 an sake shi ne awanni 48, bayan masu Garkuwa da mutane sun yi awon gaba dashi, inda aka ganshi tare da wasu mabiyan shi, a fadar shi a daran jiya Laraba.
Sarki Maude na daya daga cikin Sarakunan dake jihar Kaduna, masu yawaicin shekaru.
A wani labarin kuma
Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu ya kaddamar da yaran cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 36, domin inganta fannin kiyon lafiya a fadin jihar baki daya.
Kwamishinan fannin kiwon lafiya na jihar, Jafar Muhammad ne ya bayyana cewa, za a yi gyare-gyaren cibiyoyin kiwon lafiyan ne, a wani Shari na tseratar da rayuwar al’uma sama da milliyan daya a fadin jihar, Kuma don samun dai-daito a fannin kiwon lafiya.
” Tuni aka kammala gyaran cibiyoyin kiwon lafiya guda dari da talatin da hudu a jihar, domin inganta fannin a matakin farko” inji Kwamishinan.
” Gyaran guda 36, zai taimaka wajan farfado da fannin kiwon lafiya a matakin farko” inji shi.
Comments 2