Akalla mutane 8 ne Yan bindiga su ka yi garkuwa da su, a wani sabon hari da aka kai Agwan Fulani dake yankin Kwakwashi na jihar Niger.
Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya afku ne da musalin karfe daya na daren jiya Talata.
An Kuma bayyana cewa, Maharan sun amshi wayoyin wadanda su ka yi garkuwa da su.
Wani mazaunin yankin Mai suna Joseph Ake ya bayyana cewa, Yan bindigan sun ta yin harbe-haben, lokacin da su ka shiga yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani asibiti a Kaduna ya yi Allah Wadai da shiga yajin aikin Likitoci
Ya kuma Kara da cewa, masu garkuwan, sun yi awangaba da akalla Mutum 9 ma zauna garin, ya yin daya daga ciki ya tsere dauke da raunin harbin bindiga a jikin shi.
Ya ce ” Maharan sun zo ne da misalin karfe daya na dare, inda su ke ta harbe-harbe a sama, har lokacin da su ka fice da garin” inji shi.
“Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da Manajan wani Otel da ke yankin, da kuma wata Bakuwa da ke zaune a Otel din” a cewar shi.
Sai dai ko da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar ta Niger Abiodun Wasiu, ya tabbatar da afkuwar lamarin, amma bai yi karin haske ba kan harin.
Ya kuma kara da cewa, tuni rundunar Yan sandan jihar, ta tura Tawaga ta musamman inda lamarin ya afku, domin yin bincike, da kuma kokarin kubutar da wadanda aka sace.