Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ka wata ziyarar bazata ga shugaban jam’iyyar APC ta Kasa Bola Ahmad Tinubu a birnin Landan na Birtaniya.
Ko da yake har kawo yanzu babu wani dalili game da wannan ziyara, amma ziyarar tana zuwa ne yan kwanaki bayan da mai taimaka wa Tinubu kan yaɗa labarai ya fitar da wata sanarwar ƙaryata rahoton kamfanin jaridar Sahara Reporters nacewa Tinubu ba shi da lafiya kuma har an kwantar da shi a asibiti.
Mista Rahman ya ce Shugaban APCn yana cikin koshin lafiya, don ko dambe zai iya yi, don labarin kanzon kurege ake yadawa a kan shi.
Ya kara da cewa masu wannan jita-jita suna yi ne don irin fargabar da suke yi kan Tinubu da zarar sun ga ya yi wata ysr tafiya, inda ya ce ba ga ribar hakan ba.
Daga karshe dai ya kuma shure rade-radin mutuwar uban gidan nasa, inda ya ce bayan rai da Allah Ya yi masa, yanzu haka yana cikin koshin lafiya.