Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce wasu gungun masu safarar miyagun kwayoyi sun sace wani jami’in hukumar mai ritaya, bayan jami’an sun cafke wata ‘yar kasuwa mai safarar miyagun kwayoyi Kuma Mai suna Mngunengen Achir yar shekaru 19 a jihar Benue.
Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi, ya ce, an kama Achir ne da tabar wiwi Mai dauyin 5.5kg, da gram 112 na diazepam a ranar 6 ga watan Oktoba a yankin Aliade na jihar.
“Sauran mambobin kungiyar da aka kama sun sace Tsohon Jami’in hukumar NDLEA mai ritaya daga wannan yankin, wanda suka dauka har yanzu yana aiki ne, suka tafi da shi cikin daji suka nemi a saki wanda ake zargi a tsare, kafin a sako wanda suka kama,” in ji shi.
Babafemi ya ce, a cikin makon da ya gabata jami’an NDLEA sun kame dillalan miyagun kwayoyi 110 a jihohi tara, inda suka tarwatsa maboyarsu tare da kwace muggan kwayoyi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nuhu Ribado ya Musanta Alakanta Kowani Mutum da daukar Dauyin Yan bindiga
Ya lissafa jihohin kamar Lagos, Benue, Kwara, Ondo, Kano, Nasarawa, Akwa Ibom, Oyo da kuma jihar Rivers.
Comments 1