By Abbas Yakubu Yaura
A ci gaba da shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira na cikin gida, kwamitin jihar Borno mai kula da ‘yan gudun hijirar Baga ya tabbatar da cewa mazauna kauyukan da suka koma garin da ba kowa a baya suna zaune cikin koshin lafiya kuma rayuwar su ta ta’allaka a kansu. duk da kasancewar wasu daga cikin ‘yan ta’addan Boko Haram dake labe a yankin tafkin Chadi.
Shugaban kwamitin kuma babban lauyan gwamnatin jihar Barista Kaka Shehu Lawan ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Maiduguri a ranar Alhamis yayin da yake mayar da martani kan kalubalen dake fuskantar kudurin gwamnatin jihar na rufe dukkanin sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar nan da watan Disamba 2021.
“Mun gina gidaje sama da dari biyu na dindindin a Baga kuma mun raba wa masu su.Mun kuma gina makarantu da sauran ababen more rayuwa a fadin Doronbaga da Cross Kauwa tare da mayar da mazauna yankin gidajensu, Za mu gina asibitoci a dukkan cikin wadannan al’ummomi tare da samar musu da kayan aiki na zamani don biyan bukatun lafiyar wadanda suka dawo.
“An magance koma bayan rashin tsaro na farko duk da cewa mun san akwai sauran abubuwan da ‘yan ta’addan ke boyewa a can.
Ziyarar da zamu kai ga Kananan Hukumomin ita ce dan mu tabbatar da cewa mutanen kauyukan da suka dawo sun yi kyau,” inji Kwamishinan Shari’a.
Kaka Shehu Lawan ya ci gaba da cewa, duk da cewa al’ummar kauyen ba su fara gudanar da ayyuka kamar kamun kifi da noma ba saboda wasu kalubale na rashin tsaro, gwamnati ta hanyar kwamitin sake tsugunar da matsugunin sun fara shirin samar da filayen noma da koguna domin su tashi harkokin kasuwancin su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kimanin magidanta 8,640 da aka mayar da su garuruwan su, kakanninsu watanni uku da suka gabata sun samu tallafin abinci da kudade a garuruwan Baga, Doro da Cross Kauwa daga gwamnatin jihar Borno.sannan kuma wadanda suka ci gajiyar tallafin su 8,640,inda daga cikin 5,000 maza ne yayin da 3,640 kuma suka kasance mata ne.