An yi garkuwa da Farmat Paul, wata amarya mai jiran gado, sa’o’i kadan kafin bikin aurenta a jihar Filato.
Mazauna unguwar Ngyong da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato sun ce an sace ta ne a gidan wani faston ta inda ake sa ran za ta kwana, kafin ta wuce daurin aurenta.
Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan faston ne da misalin karfe 10:45 na dare inda suka yi awon gaba da amaryar kawai.
Wata majiya mai tushe daga iyalan amaryar ta shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, an shirya daurin auren ne a unguwar Ngyong ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Matashiya Yar Shekara 38, Ta Bayyana Aniyarta Na Maye Gurbin Shugaba Buhari A Zaben 2023
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel Ogiba, ya ce ko da yake ba a kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda ba, amma sun ji labarin kuma sun zage damtse wanjen ceto Amaryar.
Sai dai ya ce lamarin na iya yiwuwa ba satar mutane ba ne, inda ya kara da cewa “watakila ba garkuwa da amaryar aka yi ba, domin akwai lokacin da wata mata ta kwana a gidan wani mutum kuma, yayin da kowa yake zargin cewa garkuwa da ita akayi, Amma Ashe ba haka lamarin ya ke ba.
“Tun da wannan lamarin ya faru, ba a kai kara ga ‘yan sanda ba. Duk da haka, muna binciken inda take. Amma kar a yi gaggawar faɗin cewa, an Yi Garkuwa da ita nce. Mun shiga cikin lamarin.” inji Kakakin Rundunar.
A wani cigaban Kuma daga jihar ta Filato
Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya gargadi masu garkuwa da mutane da su bar jihar Filato domin duk wanda aka kama kuma aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin kisa.
Gwamnan yana magana ne a babban cocin Katolika da ke karamar hukumar Shendam a jihar.
Ya kuma tabbatar wa da ‘yan jihar cewa gwamnati za ta kara kaimi wajen yaki da duk wani nau’in laifuffuka, musamman garkuwa da mutane wanda ya zama barazana ga zaman lafiya da tsaron al’ummar jihar da ma sauran sassan kasar nan.
Gargadin bai rasa nasaba da sace-sacen da ake fama da shi a wasu sassan jihar a kwanakin baya-bayan nan ba.
A ranar 26 ga Disamba, 2021, jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da babban sarkin garin Gindiri na karamar hukumar Mangu, Charles Mato Dakat a gidansa kuma aka sake shi bayan ya kwashe kwanaki hudu a tsare.
Hakazalika, a jajibirin sabuwar shekara, an yi garkuwa da wani dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Dr Kemi Nshe a gidansa da ke garin Shendam.