Kimanin tubabbun ‘yan ta’addan Boko Haram guda takwas ne suka rasa rayukansu, daya kuma ya jikkata yayin da wani abun fashewa (IED), ya tarwatse a wani wurin zubar da shara da ke karamar hukumar Bama ta jihar Borno a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
An samu labarin cewa tsaffin ‘yan ta’addan na daga cikin mutane 800 da aka dawo da su garin Bama kwanan nan inda aka tsugunar da su a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke Bama.
Kafin faruwar lamarin Tubabbun ‘yan ta’addan da aka ce sun fito ne daga garin Bama da laifin yin mu’amala da wasu ’yan ta’addan na Boko Haram a wata kasuwa da ake kira “Daula” da ke wajen kauyen Goniri a garin Bama.
Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da yan tada kayar baya a tafkin Chadi, ya ce tsaffin ‘yan ta’addan sun karbi tarkacen daga hannun tsoffin abokan aikinsu (Boko Haram), wadanda har yanzu suke buya a dajin Sambisa ba tare da sanin cewa wasu daga cikin kayayyakin sun hada da wani bam da bai tashi ba. wanda aka yi watsi da shi bayan harin da sojoji suka kai.
Majiyar ta ci gaba da cewa, ciniki tsakanin tsoffin ‘yan Boko Haram da abokan aikinsu na baya ba wani sabon abu ba ne, inda ta ce a lokuta da dama idan suka ba su tarkace sai su rika musayar kayan abinci, kamar masara, gishiri, da Maggi da sauran su. -kayan masarufi kamar su tufafi, fetur da magunguna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Ta Gana Da Wasu Gwamnoni, Da Masu Ruwa Da Tsaki A Abuja
“Bayan sun karbi kayayyakin, za su zauna a bayan garin Bama don warwaresu su kafin su shigo da su cikin garin don sayar wa wakilansu. Suna cikin aikin warwarewar ne sai wani bam din ya tashi, inda nan take suka kashe takwas daga cikinsu yayin da daya daga cikinsu ya tsira da raunuka.