A halin yanzu dai babu wata tattaunawa tsakanin Barcelona da Manchester United kan neman Diogo Dalot.
An danganta dan wasan baya da komawa kungiyar ta Catalonia a wannan bazarar.
Dan jarida Fabrizio Romano ya ce, “Barcelona ba ta tuntubi Manchester United ko wakilin Diogo Dalot ba. An yaba shi a Barcelona amma babu wata tattaunawa da ke gudana kawo har yanzu.
“Dalot yana da daraja sosai a wurin Sabon Kocin Mancgseter United Erik Ten Hag – yayin da Aaron Wan Bissaka ya kasance ana duba yuwuwar sayar da shi kafin rufe cinikayyar yan wasan bana.”
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 300 da kayayyakin abinci a Sokoto
Hakazalika, Manchester United ta mayar da hankalinta kan Pierre-Emerick Aubameyang, Kamar yadda Jaridar The Sun ta ruwaito.
Ana alakanta Chelsea da zawarcin dan wasan gaban na Barcelona kuma tana son dawo da shi gasar Premier.
Yanzu rahotonni sun njna cewa, United na duba yiwuwar siyan tsohon dan wasan na Arsenal.
A wani labari na daban.
Hukumar zaben ƙasar Kenya ta sanar da William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar, da kashi 50.49 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Hukumar zaɓen ta sanar da sakamakon zaben ne a yammacin Litinin din nan.
An gudanar da zaɓen ne a ranar Talatar da ta gabata wato 9 ga watan Agustan 2022.
A yayin da yake jawabi bayan sanar da nasararsa, William Ruto ya ce “Yammaci ne mai matuƙar daɗi, cike da farin ciki.
Tazarar da ke tsakaninsa da abokin fafatawarsa Raila Odinga ba shi da yawa, inda shi Odingan ya samu kashi 50.4 na yawan uri’un.
An jinkirta sanar da sakamakon saboda zarge-zargen maguɗi da aka dinga yi wa ɓangaren Odinga.
Huɗu daga cikin mambobin hukumar zaɓen bakwai sun ƙi su amince da a fitar da sanarwar sakamakon, suna cewa an yi maguɗi.