An harbe wasu jami’an ‘yan sanda guda biyu a ofishinsu da ke unguwar Kuru da ke karamar hukumar Riyom a jihar Filato.
Daily trust ta rawaito cewa, ‘yan bindigar sun tafi da bindigogin jami’an da aka kashe.
Abubakar Abdulkarim, kawun daya daga cikin mamacin ya shaida wa Daily trust cewa lamarin ya faru ne a wani shingen binciken jami’an tsaro da ke kusa da Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnatin Kuru, inda ya kara da cewa an harbi dan uwansa Muktar Hassan har sau biyu sannan kuma harsashin ya makale a jikinsa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Abdulkarim ya ce an yi jana’izar Hassan, ya kara da cewa har ya mutu wanda aka kashe din yana aiki da sashin yaki da ta’addanci na rundunar ‘yan sandan jihar.