Masu garkuwa da mutanen da suka sace wani kwamishina a jihar Nassarawa, yanzu haka sun sako shi bayan ya kwashe kwanaki biyar a tsare a tare da su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kwamishinan shine na yada labarai raya al’adu da yawon bude ido na jihar Nasarawa, wato Alhaji Lawal Yakubu.
Majalisar wakilai Ta Gayyaci Wasu Ministoci Kan Rikicin Bangaren Sufurin Jiragen Sama
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Ramhan Nansel a lokacin da yake tabbatar da sakin kwamishinan a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya ta wayar tarho a ranar Juma’a, ya ce ci gaban ya biyo bayan ci gaba da matsin lamba da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi kan masu garkuwa da mutane.
DSP Ramhan Nansel ya bayyana cewa, nan take aka garzaya da kwamishinan zuwa wani asibitin da ba a bayyana ba a jihar domin duba lafiyarsa kafin ya sake haduwa da iyalansa bayan an sako shi da misalin karfe 6 na yamma.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa an tsaurara matakan tsaro a karamar hukumar Nasarawa Eggon sakamakon karuwar rashin tsaro a yankin.