Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar yada labarai ta kasa, a ranar Juma’a, ta bada umurnin rufe kafafen yada labarai 52 da suka hada da gidan talabijin mai zaman kansa na AIT, gidan talabijin na Silverbird da kuma gidajen yada labarai na gwamnatocin jihohi daban-daban ke gudanarwa da su rufe ayyukansu.
NBC ta ce umarnin ya zama wajibi ne biyo bayan basussukan da kungiyoyin yada labarai suka ci a kalla na Naira biliyan 2.6.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zan Jangoranci Fitar Da Najeriya Daga Kangin Duhun Da Take Fama Dashi — Atiku
Babban Daraktan NBC, Balarabe Ilelah ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja. Ya ce dole ne dukkanin gidajen talabijin da gidajen rediyon da abin ya shafa su dakatar da aiki nan da sa’o’i 24 masu zuwa.
Gidajen talabijin da na radiyo wadanda abin ya shafa sun hadar da;
1.Gidan talabijin na Silverbird (Silverbird Communications Co. Ltd)
2. Rhythm FM (Silverbird Communications Ltd) FM Abuja
3 Gidan Radiyo na Rhythm FM (Silverbird Communications Ltd) FM Lagos
4. Gidan Radiyo na Rhythm FM (Silverbird Communications Ltd) FM Yenagoa
5. Gidan Radiyo na Rhythm FM (Silverbird Communications Ltd) FM Port-Harcourt
6. Rhythm FM (Silverbird Communications Ltd) FM Jos
7. Rhythm FM (Silverbird Communication Ltd) Benin
8. Cibiyar sadarwa ta AIT/Ray Power FM (DAAR Communication Itd).
9. Gidan Radiyo na Greetings FM (Greetings Media Ltd) FM Network
10. Gidan Radiyo na Tao FM (Ovidi Communications Ltd) FM Okene
11.Gidan Radiyo na Zuma FM (Zuma FM Ltd) FM Suleja
12. Gidan Radiyo na Crowther FM (Crowther Communications Ltd) FM Abuja
13.Gidan Radiyo na We FM (Kings Broadcasting Ltd) FM Benin
14.Gidan Radiyo na Linksman International Itd Keffi
15.Gidan Radiyo na Bomay Broadcasting Services Itd Abuja
16.Gidan Talabijin na MTV (Murhi International Group Ltd) Ibadan
17. Gidan Radiyo na Classic FM (Pinkt Nigeria Ltd) Port-Harcourt
18.Gidan Radiyo na Classic FM (Pinkt Nigeria Ltd) Lagos
19. Gidan Talebijin Classic TV (Pinkt Nigeria Ltd) Lagos
20. Gidan Radiyo na Beat FM (Megalectrics LTD) Lagos
21. Cooper Communications Itd Lagos
22. Gidan Radiyo na Splash FM (West Midlands Ltd) Ibadan
23. Gidan Radiyo na Rock City FM (Boot Communications Ita) Abeokuta
24. Gidan Radiyo na Family FM (Kalaks Investments Nig. Ltd) Ilugun
25.Gidan Radiyo na Space FM (Creazioni Nig. Ltd) Ibadan
26. Radio Jeremi (Radio Jeremi Itd) Effurun
27.Gidan Radiyon Breeze FM (Bays Water Itd) Akure
28. Gidan Radiyo na Vibes FM (Vibes Communication Itd) Benin
29.Gidan Radiyo Family Love FM (Multimesh Broadcasting Co. Ltd) Port-Harcourt
30. Gidan Radiyo na Wave FM (South Atlantic Media Itd) Port-Harcourt
31. Kafar Watsa Labarai ta Jihar Kogi
32. Gidan Radiyon Watsa Labarai na Jiha
33.Gidan Radiyon Watsa Labarai na Jihar Neja
34. Gidan Radiyon Watsa Labarai na Jihar Gombe
35. Gidan Radiyon Watsa Labarai na Jihar Legas
36. Legas DSB
37. Gidan Radiyon Watsa Labarai na Jihar Osun
38. Gidan Radiyon Watsa Labarai na Jihar Ogun
39. Gidan Radiyo na Watsa Labarai na Jihar Ondo
40. Gidan Radiyo na Watsa Labarai na Jihar Ribas
41. Gidan Radiyo na Watsa Labarai na Jihar Bayelsa
42.Gidan Radiyon Watsa Labarai na Jihar Kuros Riba
43. Gidan Radiyo na Watsa Labarai na Jihar Imo
44. Gidan Radiyo na Watsa Labarai na Jihar Anambra
45. Gidan Radiyon Born mai Watsa Labarai na Jiha
46. Gidan Radiyon Watsa Labarai na Jihar Yobe
47. Gidan Radiyo na Watsa Labarai na Jihar Sokoto
48. Gidan Radiyo na Watsa Labarai na Jihar Zamfara
49. Kafar Watsa Labarai ta Jihar Kebbi
50. Kafar Watsa Labarai ta Jihar Jigawa
51. Kafar Watsa Labarai ta Jihar Kaduna
52. Kafar Watsa Labarai ta Jihar Katsina