Sama da ma’aikatan gwamnati 1,700 a Cross River a yau Talata sun fito kan titi don nuna rashin amincewarsu da rashin biyan albashin shekaru biyar.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa masu zanga-zangar da suka yi dandazo a sakatariyar jihar da sanyin safiyar Talata, sun tare kofar shiga sakatariyar.
A yayin da suke dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban, an hangi masu zanga-zangar suna rera wakokin hadin kai, suna masu kira ga gwamnatin jihar da ta biya su albashinsu na tsawon shekaru biyar.
KARANTA ANAN; Malaman Jami’ar FUDMA Sun Shirya Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Wasu daga cikin rubuce-rubucen da aka rubuta a allunan suna cewa: “Yunwa tana ko’ina mu mutane ne ba dabbobi ba”, “Ayade ya biya mu albashi”, “muna yin aiki yadda ya kamata, shekara biyar ba kwana biyar ba ne”.
Da yake jawabi ga manema labarai, mai magana da yawun masu zanga-zangar, Mista Raphael Antigha, ya bayyana cewa tun da aka dauke su aiki a shekarar 2017 da 2018, ba sa karbar albashi.
Ya ce su kusan 1,700 ne kuma mafi girman albashi a cikinmu shine N47,000.
Da yake mayar da martani a madadin gwamnati, shugaban ma’aikata, Mista Ogbang Akwaji, ya yi watsi da ikirarin nasu, yana mai cewa gwamnatin jihar ba wanda ya bin ta wani ta albashi.
A wani labarin kuma: Atiku Yayi Karin Haske Kan Batun Mika Ragamar Jami’o’in Najeriya Ga Jihohi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya musanta zancen da ake yadawa cewar zai mayar da jami’o’in kasar nan hannun gwamnonin jihoji.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakinsa Paul Ibe ya fitar da yammacin ranar Litinin, tare da rabawa manema labarai.