Daga: Abbas Yakubu Yaura
Majalisar hadin gwiwa ta hukumar kula da ‘yan sanda ta fitar da sanarwar yajin aikin na sai abinda hali yayi ga mahukuntan hukumar saboda saba yarjejeniyar da aka cimma.
Kungiyar ta bayyana cewa yajin aikin zai fara aiki ne daga ranar Litinin 29 ga watan Agusta, 2022. Kamar yadda Punch ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Budurwa Ta Cefanar Da Santalelan Jaririnta Kan Zunzurutun Kudi 600,000
Shugaban kungiyar ma’aikatan hadin gwiwa,reshen PSC, Mista Adoyi Adoyi, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a ranar Alhamis.
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sabani tsakanin ma’aikatan hukumar da shugaban hukumar Mista Musiliu Smith da babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Baba, kan hukumar da ya kamata ta dauki nauyin daukar ma’aikata, karin girma da kuma nada ‘yan sanda da jami’ai.
Ya yi nuni da cewa, IGP da sauran shugabannin ‘yan sanda tare da shugaban hukumar ta PSC, sun yi watsi da aikin da tsarin mulki ya ba hukumar.
Adoyi ya kara da cewa IGP ya dau alhakin gudanar da ayyukan hukumar ta PSC ba tare da mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya ba, hukuncin kotun daukaka kara da kuma mahukuntan hukumar ta PSC.
Adoyi ya ce, “Zamu fara yajin aikin ne na har sai abinda hali yayi daga ranar Litinin, 29 ga watan Agusta, domin nuna rashin gamsuwa da yadda PSC ke tafiyar da shugabancin hukumar, da kuma rashin mutunta kundin tsarin mulki, kotun shari’a. da PSC na IGO, Usman Baba.”
“Ayyukan PSC sun bayyana a cikin kundin tsarin mulki, amma IGP ya yi watsi da duk wadannan, kuma ya karbi aikin hukumar. Yana nadawa da kuma daukaka kara a lokacin da ya ga dama sabanin abin da ya zo a cikin kundin tsarin mulki.”
“Kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, nadi, karin girma, da daukar jami’an ‘yan sanda aiki ne na PSC, ba IGP ba.”Punch
A wani labarin kuma Shugaban Faransa Ya Isa Aljeriya Da Tarin Tawaga
Shugaban Faransa Emanual Macron ya isa Kasar Aljeriya a yau Alhamis inda yake fatan gyara alaƙar da ke tsakanin kasashen biyu, kasencewar man fetur da gas din da kasar ke fitarwa yana tasiri sosai ga yankin Nahiyar Turai, sakamakon fuskantar kalubale da yankin ke yi a bangaren makamashi.
BBC ta ruwaito cewa, Ziyar ta Shugaban kasar ta Faransa na zuwane bayan an dauki lokacin mai tsawo ana zaman dar dar saboda tunawa da fafutikar da kasar tayi wurin neman yanci kai wanda yayi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama.