Daga Abbas Yakubu Yaura
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC shiyyar Abuja sun kama wasu mutane 10 da ake zargi da damfara ta yanar gizo.
A wata sanarwa da kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a wani simame da aka kai a wurare daban-daban a unguwar Kubwa da Gwarimpa a Abuja bisa zarginsu da hannu wajen damfarar yanar gizo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sudan Ta Kudu Ta Kira Jami’in Diflomasiyyar Ta Da Ke Zaune A Amurka Bisa Zargin Aikata Fyade
Daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannunsu a yayin kame su akwai wayoyin hannu, kwamfutocin tafi-da-gidanka da manyan motoci guda uku- Mercedes Benz CLA 250, Mercedes Benz GLK 350 da Toyota Venza.
Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.
A wani labarin kuma Jami’o’in Jihohi A Najeriya Basu Da Amfani – ASUU
Shugaban kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana jami’o’i mallakin gwamnatocin jihohi a matsayin marasa amfani.
Farfesa Osodeke, wanda ya bayyana a gidan Talabijin na Arise a safiyar Juma’a, yana mayar da martani ne kan kudurin da wasu jami’o’in jihohi suka dauka na janye yajin aikin da kuma komawa karatu.