Daga: Abbas Yakubu Yaura
Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Abubakar Lawal, ya kama aiki a yau Juma’a a hedikwatar rundunar dake Bompai.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce manyan jami’an rundunar ne suka tarbi sabon kwamishinan.
KARANTA WANNAN LABARIN: EFCC Ta Kame Wasu Mutane 10 Da Ake Zargi Da Damfara Ta Yanar Gizo A Abuja
An tura sabon kwamishinan ‘Yan sanda zuwa Kano ranar Laraba, bayan da CP Sama’ila Shuaibu Dikko ya yi ritaya.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Dikko ya yi ritaya daga aikin ‘yan sanda a matsayin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano na 42 a ranar 27 ga watan Yuli, 2022 bayan ya cika shekaru 60 da haihuwa.
Izuwa yanzu dai tura Lawal ya zama shine kwamishinan ‘yan sanda na 43 a jihar.
Lawal wanda ya kasance haifaffen Katsina ya taba rike mukamai da dama a matsayin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Yobe da kuma DPO a sassa daban-daban na jihohin Kano da Borno da dai sauransu.
Kafin a tura shi Kano, ya kasance kwamishinan ‘yan sanda na rundunar ‘yan sandan jihar Enugu.
A wani labarin kuma Sudan Ta Kudu Ta Kira Jami’in Diflomasiyyar Ta Da Ke Zaune A Amurka Bisa Zargin Aikata Fyade
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta Kudu ta ce ta kira wani jami’in diflomasiyyar ta da ke zaune a Amurka bayan “wani lamari na fyade” a birnin New York, tare da dakatar da jami’in har sai an kammala bincike.
“Abin takaici ne cewa jami’in diflomasiyyarmu ya shiga cikin wani zargin fyade da… (a) mazaunin birnin New York,” in ji ma’aikatar a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin gwamnati na Twitter a yammacin ranar Alhamis.