Rundunar sojin Najeriya ta ce za a mika sojojin biyun da ta kora, kuma ake zargin suna da hannu wajen kashe Sheikh Goni Aisami ga rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Yobe domin gurfanar da su a gaban kotu.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Asabar.
Sanarwar ta kara da cewa an tuhumi sojojin biyu tare da yi musu shari’a a takaice saboda gaza yin aikin soja da kuma nuna rashin amincewa da horon aikin, wanda hukuncinsa a karkashin sashe na 62 (a) na dokar rundunar soji CAP A20 da sashe na 103 (1) na dokar rundunar CAP A20. Ta Tarayyar Najeriya 2004 ta tanada.
KARANTA ANAN: Japan, Da Isra’ila Zasu Hadu Don Samar Da Babur Mai Amfani Da Hasken Rana A Najeriya
Sanarwar ta ce an same su da laifukan da ake zargi, duka biyun kuma an rage musu matsayi daga Lance Corporal zuwa na masu zaman kansu da kuma korarsu.
Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, mukaddashin kwamandan bataliya ta 241, dake Nguru, Laftanar Kanal Ibrahim Abdullahi Osabo ya ce, “ba shakka wadannan mutane (sojojin da aka kora) ba za su taba wakiltar mu ba.
Ana biyan mu kudaden masu biyan haraji na Najeriya mu rike bindigogi mu kare kasar nan, amma abin da wadannan sojoji suka yi, gaskiya ba ya daga cikin sharuddan aikin sojojin Najeriya.”
Idan dai za a iya tunawa, rundunar sojin Najeriya ta yi alkawarin kafa wata hukumar bincike domin bankado al’amuran da suka faru tare da gaggauta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya don fuskantar hukunci daidai da abinda suka aikata.
A wani labarin kuma: Cikar Jihar Enugu Shekaru 31: Gwamna Ugwuanyi Ya Yabawa Iyayen Da Suka Kafata
Gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ya taya Al’ummar jihar murnar cika shekaru 31 da kafuwarta tare da nuna matukar godiya ga iyayen da suka kafa ta bisa hangen nesa da karewa da jajircewarsu wajen samar da jihar.
Da yake kwatanta iyayen da suka kafata a matsayin “jarumai na gaskiya”, gwamnan ya ba su tabbacin cewa sadaukarwar da suka yi ba za ta kasance a banza ba.