Tsohon shugaban tarayyar Soviet wanda ya kawo karshen yakin chahar baka Mikhail Gorbache ya rasu yana da shekaru 91. Kamar yadda BBC ta ruwaito
Mista Gorbache ya jagoranci Tarayyar Turai ne a alif dari tara da tamannin da biyar 1985 in da ya kawo wasu sauye- sauye tare da fitar da tarayyar Soviet a fadin duniya.
Sai dai mafi yawaicin yan kasar Rasha na ganin ya gaza dakatar da rugewar tarrayar ta Soviet.
A kasashen duniya da ban daban-daban ana girmama shi sosai inda ake ganinsa a mastayin wanda ya kafa wani tarihi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kano: Duk Wata Ana Kwashe Tifar Shara 1,500 Don Gujewa Matsalolin Muhalli – Getso
A wata takardar jajantawa da ya fitar , Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana Mikhail Gorbachev a matsayin dan kishin kasa.
Ya bayyana shi a matsayin wanda bai nuna gajiyawa wurin neman zaman lafiya, Anotonio yace duniya ta rasa wani babban jigo.
A watan Yuni ne manyan kafafen yaɗa labarai na duniya suka rawaito cewa an kwantar da mamacin a assibiti saboda matsalar cutar ƙoda da ya kamu da ita, koda yakehar kawo hada wannan rahoton ba’a bayyana dalilin mutuwar sa ba.
Za’a dai binne shi ne a wata maƙabartar da ake rufe wasu fitattun mutane a birnin Mascow da ake kira Novodevichy.
Shima Shugaban Rasha Vladimir Putin ya aike da sakon ta’aziyarsa ga iyalan marigayin, inda ya bayyana irin tasiri ,da irin gudunmawar da Mista Gorbache ya bayar.
Shugaban ya ce Gorbache ya fahimci akwai buƙatar yin wasu sauye-sauye dake da suke da muhimmanci sosai don tunkarar magance kalubalen da ake fuskanta a wancan lokaci.
Sai dai dangantakarsu tayi tsami tun haɗuwar su a shekarar 2006.
A baya bayyanan an tabbatar da cewa Gorbache baiji daɗin matakin da Putin ya ɗauka na mamayar kasar Ukraine ba, koda yake ya goyi bayan karɓe yankin Crimea daga Ukraine da ƙasar tayi a shekarar 2014.
Anashi bangaren, A cikin sakonsa na karramawa da jajantawa Firamiinistan Birtaniya Boris Johnson ya yaba da jaruntaka da amincin Mista Gorbachev.
Shima da yake nashi tsokacin, Shugaban Amurka Joe Biden ya kira Marigayin da shugaban da ba kasafai ake samun irinsu ba.
Ya kuma yaba wa Mista Gorbachev inda ya bayyana shi a matsayin fitaccen dan siyasa wanda ke da hangen nesa wurin cimma wata makoma ta daban a lokacin da ake tsaka da yakin cacar baka.
Kazalika, anata sakon, shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta yaba masa tare da bayyana shi a matsayin amintaccen shugaba kuma mai mutuntawa wanda ya baiwa Turai yanci da dama.
A WANI LABARIN KUMA: Ka Tabbata PDP Tayi Nasara A Kano, Jigawa, Kaduna Da Neja, Saƙon Wike Ga Makarfi
Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bukaci tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ahmed Makarfi da ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta yi nasara a jihohin Arewa.
Wike yace ya kamata Makarfi ya tabbatar da cewa PDP tayi nasara a jihohin Kano, Jigawa, Niger, da Kaduna.