Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bukaci matasa da su yi watsi da masu kokarin raba kasar da siyasar kabilanci da addini gabanin zaben 2023.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Owerri a wajen taron cika shekaru 80 na Cif Emmanuel Iwuanyanwu.
Karanta kuma: 2023: Ku Sanya Nijeriya A Gaba – Jonathan Ga Ƴan Siyasa
Jonathan ya lura cewa siyasar Najeriya ta kunno kai cikin kabilanci da addini “don cutar da kasarmu da kuma tushenmu. Ina ganin ya kamata mu rage wannan.”
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ya kara da cewa: “A dunkule, idan muka hada kai muka daidaita sabanin dake tsakaninmu, za mu iya gina kasa da kowa zai san nasa. Kuma za a tabbatar da hakkin kowa.
“Hakan ya kamata mu bi – Najeriya inda adalci, gaskiya da daidaito ke mulki.”
A wani labarin kuma: Yanzu Najeriya ce ƙasa ta biyu data fi kowace ƙasa fama da ta’addanci- Jihad Analytics
Kungiyar Binciken Ta’addanci ta Duniya, wato Jihad Analytics, ta ce Najeriya yanzu ita ce kasa ta biyu da kungiyar ta’addanci mai rajin Kafa ƙasar musulunci ke addaba a faɗin Duniya.
Ƙungiyar Bincike kan Jihadi ta ƙware wajen tattara bayanai kan ayyukan ta’addanci a Duniya.