Chelsea ta tabbatar da cewa, ta kammala daukar Graham Potter a matsayin sabon kocinta.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis da yamma, Blues ta bayyana cewa tsohon kocin Brighton ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar a Kunguyar.
Daily Post ta ruwaito cewa, Potter ya maye gurbin Thomas Tuchel wanda aka kora jiya jiya ta hannun mamallakin The Blues, Todd Boehly.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: PDP Ta Nada Wabara A Matsayin Sabon Shugaban BoT Na Jam’iyyar
A kan komawa Chelsea, Potter ya ce: “Ina matukar alfahari da zama sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea FC, wannan babbar kungiyar kwallon kafa ce.
“Na yi matukar farin ciki da yin aiki tare da sabon rukunin mallakar Chelsea kuma ina fatan zamu yi aiki tare da rukunin ‘yan wasa masu ban sha’awa da haɓaka ƙungiya waɗanda magoya bayanmu masu ban mamaki za su yi alfahari da ita.
“Ina kuma so in mika godiya ta ga Brighton & Hove Albion saboda ba ni wannan dama musamman Tony Bloom da dukkan ‘yan wasa, ma’aikata da magoya bayana saboda ci gaba da goyon bayan da suke yi a lokacin da nake kulob din.”inji sabon kocin
A WANI LABARIN KUMA: Shugaban Karamar Hukumar Da Akayi Garkuwa Da Shi A Filato, Ya Shaki Iskar Yanci
Shugaban karamar hukumar Kanke ta jihar Filato, Henry Jan Gotip, ya shaki iskar Yanci kwanaki kadan bayan yan bindiga sun yi garkuwa da shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred ne ya tabbatar wa manema labarai sakin wanda shugaban, ya kuma kara da cewa an sako Henry ba tare da jin rauni ba a daren jiya Laraba.