Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta aiwatar da aikin samar da wutar lantarki na Mambilla a jihar Taraba.
Sun yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwar da suka fitar a karshen taron su na bakwai da suka gudanar a karshen mako a gidan gwamnatin Gombe a jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe sun yi taro a Gombe domin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi yankin da kuma kasa baki daya.
KARANTA KUMA: Wasu Gwamnonin Arewa Sun Bukaci Kafa Yan Sandan Jihohi
A cikin sanarwar da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya karanta a karshen taron, sun nuna damuwarsu kan halin da wutar lantarki ke ciki a yankin Arewa Maso Gabas.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Buni ya ce Jihohin shida na karbar kashi biyar cikin dari na kudin wutar lantarki na kasa yayin da su ke da kashi 14 cikin 100 na al’ummar kasar da kuma kashi 30 na fadin kasar.
Ya yi nuni da cewa, akwai alaka kai tsaye tsakanin makamashi, tsaro da matsanancin talauci da kuma babban abin da ake samu a cikin gida (GDP).
“Saboda haka, NEGF, ta bukaci Majalisar ‘Yan Kasuwa ta Arewa Maso Gabas da ta farfado da kasuwar hada-hadar kasuwanci ta Arewa maso Gabas da kasuwannin kayayyaki don zaburar da harkokin tattalin arziki,” in ji sanarwar.
Gwamnonin sun kuma bayyana damuwarsu kan yadda yankin ke kara fuskantar tabarbarewar tsaro sakamakon yawaitar ‘yan bindiga da sannu a hankali jami’an tsaro ke fatattakar su daga yankin na Arewa maso Yamma.
Taron ya yi kira da a gaggauta kaddamar da taswirar tsaro tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya domin duba kwararar ‘yan fashin.