Mai shari’a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin din nan ya yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar na neman a soke takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu da na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi bisa zargin sauya abokan takarar su ba bisa ka’ida ba.
Alkalin ya ce PDP tana da nufin tada hankalin abokan hamayya a zaben shugaban kasa na 2023.
Mai shari’a Okorowo ya bayyana cewa karar da wani babban Lauyan Najeriya, SAN, Gordy Uche ya shigar a madadin jam’iyyar PDP bai dace ba kuma babu hujja domin bai bayyana wani dalili na daukar mataki ba.
KARANTA KUMA: PDP Ta Bukaci Kotu Ta Hana Inuwa Yahaya Takara A Zaben 2023
Baya ga haka, alkalin ya ce PDP ta kasa bayyana duk wani rauni da ta samu wajen sauya ‘yan takarar APC da Labour Party suka yi.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, ‘Yan takarar da PDP ke kalubalantar maye gurbinsu da suka hada da Kabiru Masari da Doyin Okupe na APC da Labour Party.
A cikin karar, PDP ta yi ikirarin cewa dokar zabe ta 2022 ba ta yi tanadin “mai rike da mukami” ko abokin takara na wucin gadi ba, janyewa ko sauya ‘yan takarar shugaban kasa na gudanar da sabon zaben fidda gwani don maye gurbinsu bai dace da Masari ba da Okupe.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa, PDP ta kuma ce Tinubu da Obi za su iya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 tare da Masari da Okupe a matsayin abokan takararsu.
Sai dai alkalin ya ce batun nadawa da sauyawa al’amuran cikin gida ne na jam’iyyu don haka kotuna ba ta da hurumin shiga cikin su.
Wadanda ake karar da suka shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1016/2022 sun hada da INEC, APC, Bola Ahmed Tinubu, Kabiru Masari, Labour Party, Peter Obi da Doyin Okupe na 1 zuwa 7.
A wani labarin kuma: Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Jana’izar Sarauniya Elizabeth
A halin yanzu ana ci gaba da jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu.
Ana gudanar da jana’izar Sarauniyar wacce ita ce sarki mafi dadewa a kan karagar mulki a birnin Landan.