Ku tabbatar anyi Zaɓen 2023 cikin Zaman Lafiya – Kiran Limamai ga Ƴan Siyasa
Majalisar Limamai da Malamai reshen Jihar Kaduna, ta yi kira ga ƴan siyasa da Musulmi baki daya da su gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali ba tare da nuna kyama ba, a daidai lokacin da ake fara yakin neman zaben 2023.
Mataimakin Babban Sakatare-Janar Imam Musa Tanimu da jami’in hulda da jama’a na majalisar, Dokta Abdullahi Maikudi, a wani taron Manema Labarai na haɗin gwiwa, jiya a Kaduna, sun kuma yi kira ga ‘yan kasar da su guji maganganun da ka iya haifar da karya doka da oda.
KARANTA WANNAN LABARIN: Iyaye sun koka kan Dakatar da shirin ciyar da abincin Ƴan Makaranta a Zamfara
Majalisar ta ce tana aiki ne da ajandar ganin an gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali, wanda za a bayyana shi ga al’umma baki daya.
“Saboda haka, majalisar tana kira ga mambobinta da su yi taka-tsan-tsan tare da guje wa irin wadannan jarabawowin, wanda kawai burinsu shi ne wargaza dangantaka ta dindindin da kuma dorewa a tsakanin mambobin.
Hakazalika, Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Al’ummar Musulmi ta Jihar Kaduna, Dakta Yusuf Arigasiyyu, ya bukaci al’ummar Musulmi da su zabi fitattun shugabanni masu kishin kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Da yake jawabi a lokacin da wasu kungiyoyin musulmi suka kai masa ziyarar ban girma, ya bukace su da su kara himma wajen wayar da kan musulmi su fito su zabi shugabanni na gari.
A wani labarin kuma: An yiwa Mai Gadin Kasuwar Jos yankan Rago
An gano wani mai gadi mai suna Muhammad Kabiru da aka yanka a kasuwar Dare, wani sashe na kasuwar Jos Ultramodern Market da sanyin safiyar Asabar.
Mahukuntan kasuwar sun ce marigayin wanda mai gadi ne a kasuwar ya ce an kashe shi ne da tsakar dare a wurin aikinsa yayin da aka tsinci gawarsa a kusa da kasuwar.