An yiwa Mai Gadin Kasuwar Jos yankan Rago
An gano wani mai gadi mai suna Muhammad Kabiru da aka yanka a kasuwar Dare, wani sashe na kasuwar Jos Ultramodern Market da sanyin safiyar Asabar.
Mahukuntan kasuwar sun ce marigayin wanda mai gadi ne a kasuwar ya ce an kashe shi ne da tsakar dare a wurin aikinsa yayin da aka tsinci gawarsa a kusa da kasuwar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Manomi Ya Nutse a Ruwa, Yayin da Mutane 8 Suka tsira a Hatsarin Kwale-kwale
Shugaban Kasuwan Dare, Alhaji Jamilu Kabiru, a lokacin da yake zantawa da Daily Trust game da lamarin, ya ce, “An samu an kashe jami’in tsaron mu, daya daga cikin masu karfi kuma amintacce a kasuwar.
“Daya daga cikin abokan aikina ne ya kira ni da safe ranar Lahadi domin in ga gawar. Lalle ne babban abin bakin ciki ne kuma babba. Mun kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.”
Ya ce marigayin ya yi aikin gadi a kasuwar tsawon shekaru 15 kuma ba su taba samun matsala da shi ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu wajen gudanar da kisan.
Alabo ya ce, “DPO na yankin ya fara aiki kan lamarin. Saboda yanayin lamarin, an kama wasu mutane bakwai da ake zargi. Ana ci gaba da binciken.
A wani labarin kuma: Iyaye sun koka kan Dakatar da shirin ciyar da abincin Ƴan Makaranta a Zamfara
Iyaye da masu kula da Ɗaliban Makarantun Gwamnatin jihar Zamfara sun koka da yadda gwamnatin jihar ta dakatar da ciyar da dalibai kyauta, wanda hakan zai hana Ɗaliban shiga makarantun gwamnati.
Sun yi nuni da cewa, ciyar da yara kyauta yana da tasiri mai kyau wajen habaka ilimi, domin yana kara wa dalibai kwarin guiwa su kasance a kan lokaci a makarantun.