Dubban matasa ne a ranar Asabar suka yi dafifi a Legas domin taron gangamin mutum miliyan 4 na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Magoya bayan sun bijirewa dokokin da aka sa a safiyar ranar da kuma tsaro na gudanar da taron a sassan Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Alamun Fili Dana Ɓoye Sun Tabbatar Da PDP Zata Kwace Najeriya A 2023 – Atiku
An gudanar da gangamin ne a lokaci guda a Ikeja, FESTAC, Surulere, Lagos-Island-Lekki axis inda matasa da dama suka yi dandazo domin nuna goyon bayansu ga takarar Obi wanda suka ce har yanzu shine wanda sukeso ya zama shugaban kasa kasar.
Daily Trust a ranar Lahadin ta ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Legas a baya ta hana magoya bayan Obi da aka fi sani da Obi-dients yin taro a Lekki Tollgate domin gudanar da tattakin.
Duk da dimbin jami’an tsaro a Tollgate, wakilin majiyar Dimokuradiyya ya lura da cewa magoya bayan sun bi ta kan titin ne suka nufi Lekki kai tsaye.
Wannan lamari dai ya haifar da cunkoso mai yawa a babban titin Lekki-Epe mai cike da zirga-zirgan ababen hawa
Olisa Emeka, daya daga cikin magoya bayan Obi wanda ya zanta da wakilin Majiyar Dimokuradiyya a Ikeja, ya ce goyon bayansa ga Obi ya ta’allaka ne a kan imaninsa da cewa yana da karfin da kuma gaskiyar ci gaban Najeriya a tsakanin sauran ‘yan takarar shugaban kasa.
A WANI LABARIN KUMA: Bani Da Wani Gilla A Zuciyata Dangane da Shugaba Buhari – Gwamna Ortom
Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya ce ba shi da wani abu na kashin kansa da zai yi amfani da shi domin sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya bayyana cewa yana sukar shugaban kasa ne kawai kan rashin iya kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar da kuma Najeriya.