Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya ce ba shi da wani abu na kashin kansa da zai yi amfani da shi domin sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya bayyana cewa yana sukar shugaban kasa ne kawai kan rashin iya kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar da kuma Najeriya.
Gwamnan ya mayar da martani ne ga jawabin Shugaban kwamitin kula da ilimin Manyan Makarantu na Majalisar Wakilai, Aminu Suleiman Goro yayi tare da yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a lokacin kaddamar da wasu ayyuka a Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Makurdi.
KARANTA ANAN: Wata Babbar Ɓaraka Na Neman Kunno Kai Tsakanin Tinubu Da Wasu Jiga Jigan APC
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa shugaba Buhari ya roki gwamna Ortom da ya yi kokarin amincewa da manyan ayyukan gwamnatinsa a jihar Benuwe maimakon yi masa zagon kasa.
Amma Gwamnan a jawabinsa a ranar Asabar, 1 ga Oktoba, 2022 ya ce gwamnatin jihar ta shirya tare da kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ya jaddada cewa ba shi da wani abu na kashin kansa a kan shugaban kasa face ya damu da kashe-kashen da ake yi wa al’ummarsa.
Taron ya gudana ne a cocin Faith Cathedral of All Nations Evangelism Ministry, Old GRA, Makurdi.
A wani labarin kuma: Dole Kowace Jam’iyya Ta Faɗi Hanyar Da Ta Sami Kudin Kamfe – INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce dole ne jam’iyyun siyasar kasar nan su bayyana hanyoyin da suka samu kudaden yakin neman zabensu tare da kiyaye ka’idojin da suka shafi kudaden yakin neman zabe da kayyade kashe kudade.
Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wata hira ta musamman da yayi da gidan talabijin na Trust TV.
A cewarsa, akwai kuma iyaka ga abin da daidaikun mutane za su iya ba da gudummawar don ba da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe, saboda daidaikun mutane ba za su iya ba da gudummawa kawai ba bisa ƙayyadaddun iyaka.