Tsohuwar jaruma a masana’antar Kannywood, Ummi Rahab kuma mata ga jarumi, mawaki kuma furodusa, Lilin Baba ta bayar da albishir mai dadi kamar yadda Fim Magazine ta ruwaito.
A cewarta, Ubangiji ya albarkaceta da samun juna biyu, don haka tana fatan za a sanya mata albarka a wannan karuwar da ta samu.
Kamar yadda rahoton ya nuna, ta shaida hakan ne a shafinta na Instagram inda ta shaida da harshen turanci.
“Na samu ciki. Kuma zan bayar da kyautar kati ga duk mutane 50 na farko da su ka taya ni murna.”
Tuni jama’a su ka bazama su na taya ta murnar karuwar da ta samu tare da angon nata, inda su ka dinga tsokaci karkashin wallafar.
Duk da dai jarumar ba ta bayyana yawan kyautar da za ta bayar ba, amma da alamu tana cikin farinciki.
Idan ba a manta ba, an daura auren jarumar da angon nata ne ranar 18 ga watan Yunin 2022 a Tudun Murtala da ke cikin garin Kaduna akan sadakin aure N200,000.
Har ila yau, Jarumi Ali Nuhu ne ya kasance waliyyin ango inda ya amsa masa auren kyakkyawar amaryar ta shi.
KU KARANTA: Auren Zahra Diamond da cire Ummi Rahab, mecece makomar fim din Farin wata?
A yanzu dai za a iya cewa kallo ya koma sama, dangane da fim din da Adam A Zango ya ke shirya wa mai dogon Zango wato “Farin Wata Sha Kallo” a sakamakon cire Ummi Rahab da kuma auren ba zata da ita ma jarumar fim din Zahra Diamond ta yi, ana dab da fara ci gaban aikin.
Ga duk masu kallon fim din dai, za su gane wadannan jaruman biyu a kan su labarin ya ke tafiya, domin labarin ya dakko ne daga lokacin da Ummi Rahab ta ke karama, idan ta girma ta ke zama Zahra Diamond, to ana tsaka da fim din aka yi rabu war Dutse hannun riga tsakanin Adam A Zango da Ummi Rahab, kuma ita ma Zahra Diamond, da ta tafi garin su a Jamhoriyar Niger, da shirin za ta je gida ta yi babbar Sallah ta dawo, sai kawai aka ga ta aiko da sakon ta yi aure, don haka ta na bai wa duk wanda ta ke cikin fim din sa hakuri, domin ba za ta samu damar ci gaba ba, saboda ta yi aure, don haka tana yi musu fatan alheri.