A safiyar yau ne mutanen Kano suka tashi da alhinin rasuwar Malam Falalu Dan Almajiri. Kafin rasuwar Malamin ya kasance shugaban majalisar Limaman jihar Kano.
Dan Almajiri ya yi jinya ta tsawon lokaci, a jiya ne da misalin karfe 1 na dare aka yi masa aiki wanda daga bisani Allah ya karbi rayuwarsa, kafin rasuwar tasa ana zargin malamin ya kamu da ciwon jeji ne.
Sheikh Dan Almajiri ya tafiyar da rayuwarsa wajen bawa addinin Allah gudunmawa ta hanyar koyar da dalibansa.
Walikinmu ya samu damar tattaunawa da daya daga cikin ‘Ya’yan Malamin, wato Bashir Falalu, ta wayar Salula, inda ya shaidawa wakilin namu cewa za a yi Ja’izar mahaifin nasu da misalin karfe 2 na rana dake gidansa a layin ‘Yan Kabalu a karamar Hukumar Fagge dake Kano. Za a birne Malamin ne a Makabartar dake kan titin zuwa Hajj camp dake a cikin birnin Kano.
Muna fatan Allah ya jikan malamin, ya kyautata makwancinsa, amin.
Daga: Abubakar Muhammad Usman