A ranar Alhamis ne aka gurfanar da Adelekan Aderemi dan shekaru 38 da haihuwa a gaban kotun Majistiri dake zaman a Ile-ife bisa lafin barazanar kashe mahaifinsa Adewale Aderemi.
Wanda ake hutumar ana zarginsa da yiwa mahaifinsa baraza da barin fasasshiyar kwalba, biyo bayan sabani da suka samu.
Jami’in dan sandan dake kula da lamarin ya shaidawa kotu, cewa Adelekan ya aikata laifin ne a ranar 1 ga watan nan da muke ciki a titin Iremo dake Ile-ife.
Ya kara da cewa mai laifin ya aikata tada zaune-tsaye ne.
Yace mai laifin ya shiga gidan mahaifinsa wanda akwai mai gadi amma yake yiwa mahaifin nada baraza da barin fasasshiyar kwalba.
https://dimokuradiyya.com.ng/saurin-fushi-kotu-ta-yankewa-wani-hukuncin-kisa-sakamakon-kashe-mahaifinsa/
Laifin nasa ya saba da kudin laifuka karkashin sashi na 249(D) na kudin laifuka na jihar Osun na Shekarar 2002.
Sai dai Adeleken ya musanta zargib da ake masa na aikata laifin.
Sai dai lauyan da yake kare wanda ake tuhumar Martin Awe, ya roki kotu da ta bada belinsa kafin zama na gaba.
Alkalin kotun Joseph Owolawi ya dage karar zuwa ranar 25 ga watn Yunin da muke tare da bada belin wanda ake zargin akan kudi Naira dubu 100,000 tare da sharadin gabatar da mutum daya da zai tsaya masa.